MUN GODEWA ALLAH DA YA BAI WA Eng. ABBA KABIR NASARA A KOTUN KOLI-SHUGABAN SUBEB

Daga JB Danlami
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir ya taya Zababben Gwamnan Jiha Eng Abba Kabir Yuisf murnar samun nasa a kotun kolin zabubbukan Gwamna.
Malam Yusif Kabir ya bayyana murnar ta sa cikin wata sanarwa mai dauke da Sanya hannun mai magana da yawun Hukumar Balarabe Danlami Jazuli.
Shugaban ya godewa Allah madaukakin sarki bisa bayyana gaskiyar lamari inda abun alumma suka zaba shi ne tabbata a kotun.
“Muna godewa Allah bisa wannan nasara da alumma Jiha suka samu domin kuwa nasarar kowa da kowa ce”‘ in ji Malam Yusif.
Daga bisani Shugaban Hukumar, ya bukaci daukacin alumma, su bai wa Gwamnatin Abba Kabir Yuisf goyon baya don ya samu damar gudanar da ayyukan alheri ga daukacin alumma Jiha.
Har ila yau Malam Yusif ya yi wa alummar jihar nan albishir na cewa, Gwamnatin Abba Kabir ta yi tanadin managertan tsare tsare da za su inganta ilimi.




