ZAMU BAYAR DA FIFIKO WAJEN KAI ZIYARA MAKARANTUNMU-SHUGABAN SUBEB

Daga JB Danlami
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir ya bayyana cewa, Hukumar ta yi tanadin hanyoyin karrama malamai masu zuwa aiki kan lokaci, kazalika Hukumar zata hukunta malaman da aka samu da hallayar makara ko kin zuwa aiki.
Malam Yusif Kabir, ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara aiki a wasu makarantu da suke yankin Karamar Hukumar Gwale.
Da yake jawabi ga Malamai da Daliban Makarantar Firamare ta ‘Yan mata ta Dukawuya Model science da na Makarantar firamare ta Dukawuya Model ya nuna gamsuwarsa bisa yadda malaman makarantun da dalibansu suke zuwa makaranta kan lokaci, tare da jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu.
A bangare guda kuwa, Malam Yusif Kabir ya nuna bacin ransa bisa samun yawaitar makara daga malamai da daliban makarantar firamare ta Dorayi babba sai ya hore su da su sauya wannan dabi’a tun kafin hukumar ta dauki matakin ladaftarwa a kansu.
Kazalika, shugaban Hukumar ya umarci sakataren ilimin yankin da ya hanzarta rage yawan mataimakan shugaban makarantar firamare ta Dukawuya daga uku zuwa biyu a wani mataki na inganta ayyuka a makarantar.
Bugu da kari, Malam Yusif Kabir ya bukaci Kwamitin Alumma gatan (SBMC) makaranta na makarantar ta Dukawuya su bullo da hanyoyin wayar da kan iyaye don sanya ‘ya ‘yansu a makaranta tare da tabbatar da zuwansu kan lokaci.
Da bisani Malam Yusif Kabir ya bukaci alummar jihar nan su ci gaba da marawa tsare-tsare da manufofi Gwamnatin injiya Abba Kabir Yuisf don ta samu damar cika burinta na ingamta rayuwar alumma musamman a fagen bayar da Ilimi.



