Za a Kaddamar da Shirin Ɗaukar Sabbin Daliban Firamare na Shekarar 2025/2026 a Masarautar Rano
Daga JB Danlami
Da yake sanar da Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Isa Umar, a fadarsa game da wannan shiri, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano, Malam Yusif Kabir, wanda ya samu wakilcin Kwamishina na Ɗaya na Hukumar, Hon. Wada Ibrahim Daho, ya bayyana cewa sakamakon zaɓen Jihar Kano da Hukumar Ilimin Bai Daya ta Ƙasa ta yi a matsayin jiha da za a kaddamar da shirin, Hukumar a matakin jiha ta yanke shawarar gudanar da kaddamarwar a Masarautar Rano.

Ya ƙara da cewa zaɓin da aka yi wa Masarautar Rano ya biyo bayan la’akari da irin gudunmawar da Sarkin Rano yake bayarwa ga ci gaban ilimi.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Isa Umar, wanda ya samu wakilcin Madakin Rano, Alhaji Addau Isa, ya bayyana cewa masarautar a shirye take wajen tallafa wa duk wani shirin wayar da kan al’umma domin su sanya ‘ya’yansu a makaranta, don samun ingantacciyar al’umma.
Shi ma da yake maraba da ayarin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Hon. Naziru Yau Rano, ya gode wa Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha, Malam Yusif Kabir, bisa zaɓar yankin don kaddamar da shirin ɗaukar sabbin daliban firamare na shekarar 2025/2026.

Haka kuma, ya bayyana godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, bisa bijiro da shirye-shiryen raya ilimi, tare da bayyana kudurin ƙaramar hukumar wajen yin duk abin da ya kamata don samun nasarar shirin.




