An zabi Shugaban SBMC na Kano a matsayin Shugaban Kwamitin SBMC na Shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan.
An zabi Shugaban SBMC na Kano a matsayin Shugaban Kwamitin SBMC na Shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan.

An zabi Shugaban SBMC na
Kano a matsayin Shugaban Kwamitin SBMC na Shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan.
Daga JB Danlami
A wani mataki na samar da Shugabancin Kwamitin SBMC na kasa Hukumar Ilimin Bai Daya ta kasa UBEC ta tsara gudanar da zubukan kwamitocin a matakin shiyyoyin kasar nan.
Bisa masalaha wakilan Jihohin Shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan sun amince da zaban Tijjani Haladu Baraya a matsayin Shugaban Shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan.
Shugabanim da aka zaba daga shiyyoyi sune suka tsara yadda aka fidda Shugabanci na matakin kasa.
A jawabansa Jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben sabon Shugaban Kwamitin SBMC na Shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan Kuma Shugaban Kwamitin SBMC na Jihar Kano Alh Tijjani Haladu Baraya ya nuna godiya ga Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha Malam Yusif Kabir bisa yadda ya taimakawa ayarin wakilan Jihar Kano su halarci wannan taro.
Kazalika ya bayyana aniyar Kwamitin wajen lalubo hanyoyin hada hannu da sauran ma’aikatun da suke da nasaba da harkokin Ilimi don inganta hanyoyin shigar alumma a harkokin tallafawa Ilimi
A zabe da aka gudanar nà Shugabancin Kwamitin SBMC na matakin kasa kuwa an zabi Alhaji Abdullahi Umar Wazirin Gwandu daga Jihar Kebbi a matsayin Shugaban SBMC na kasa inda Kuma Dr. Ashir Ismail daga Jihar Legos ya zama Sakataren Kwamitin na kasa.
.




