Zamu hada hannu da duk wata KH dake da nufin bunkasa harkokin Ilimi-Shugaban SUBEB
Zamu hada hannu da duk wata KH dake da nufin bunkasa harkokin Ilimi-Shugaban SUBEB

Daga JB Danlami
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha, Malam Yusuf Kabir, ya jaddada kudurin hukumar na yin aiki tare da kananan hukumomi domin inganta harkokin ilimi a fadin jiha.
Malam Yusuf Kabir ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Shugaban Karamar Hukumar Gaya, Hon. Mahmud Tajo Sani, wanda ya jagoranci daukacin kansilolin karamar hukumar zuwa ziyarar aiki a harabar hukumar dake Sakatariyar Audu Bako.
A jawabinsa, Malam Yusuf Kabir ya bayyana cewa gwamnatin jiha tana kokarin bunkasa fannin ilimi ta hanyar gina sabbin ajujuwa, gyara wasu da dama, da samar da kujerun zama a makarantu, da kuma samar da kayan koyo da koyarwa. Haka nan, gwamnatin na kuma kokarin inganta walwalar malamai domin su ci gaba da bayar da gudunmawa ga ilimin yara.
Shugaban hukumar ya nanata cewa, duk da irin namijin kokarin da gwamnatin jiha ke yi, akwai bukatar shugabannin kananan hukumomi su dauki nauyin aiwatar da ayyukan raya ilimi a yankunansu.
Ya gode wa Shugaban Karamar Hukumar Gaya bisa nuna jajircewarsa ga harkokin ilimi da kokarinsa na bunkasa ilimi a yankinsa.
Haka kuma, ya bukaci sauran shugabannin kananan hukumomi su yi koyi da irin tsare-tsaren inganta ilimi da karamar hukumar Gaya ke aiwatarwa.
A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Gaya, Hon. Mahmud Tajo Sani, ya bayyana cewa sun kai wannan ziyarar ce domin mika godiyarsu ga Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa irin ayyukan raya ilimi da gwamnatin jiha ke aiwatarwa a yankin.
Ya kara da cewa karamar hukumar Gaya ta amfana da sabbin gine-ginen ajujuwa, samun kujerun dalibai da na malamansu, da kuma kayan sawa na makaranta ga dalibai. Bugu da kari, sun kuma samu kayan koyo da koyarwa domin inganta harkokin ilimi a yankin.
Hon. Mahmud Tajo Sani ya kuma bayyana cewa karamar hukumar Gaya ta tsara jadawalin ci gaban ilimi a yankin domin tabbatar da ci gaba mai dorewa a fannin ilimi.



