Education

SUBEB Za Ta Raba Kujerun Dalibai 31,363 da Kujerun Malamai 1,570 ga Kananan Hukumomi 31

SUBEB Za Ta Raba Kujerun Dalibai 31,363 da Kujerun Malamai 1,570 ga Kananan Hukumomi 31

Daga JB Danlami

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB), Malam Yusuf Kabir, ya bayyana cewa Hukumar ta kammala shirye-shiryen raba kujerun zaman ɗalibai guda 31,363 da kujerun malamai guda 1,570 ga Kananan Hukumomi 31 na jihar domin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantu.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar duba wuraren da ake ƙera kujerun a kan Titin Zariya da kuma Titin Maiduguri.

Da yake yaba wa ingancin aikin, Malam Yusuf Kabir ya ce waɗannan kujeru ƙari ne kan kujeru 16,903 da Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samar tare da rabawa Kananan Hukumomi 13 a baya.

Ya ƙara da cewa, baya ga kujerun ɗalibai, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma amince da samar da kujerun malamai domin ba su damar gudanar da aikinsu cikin yanayi mai kyau.

Shugaban ya ce an tanadi waɗannan kujeru ne domin rabawa makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandare da ke fama da ƙarancin kujeru.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa Hukumar za ta ci gaba da samar da kujeru ga sabbin makarantu da kuma waɗanda aka gyara.

A wani ɓangare na ziyarar tasa, Malam Yusuf Kabir ya jagoranci jami’an Hukumar zuwa Ƙaramar Hukumar Garun Mallam, inda suka duba ayyukan gyaran Makarantar Firamare ta Ringimawa, Makarantar Firamare ta Samawa da kuma Makarantar Firamare ta Ciromawar Idi.

Da yake a  Makarantar Firamare ta Samawa, Shugaban ya yi kira ga al’ummar yankin da su ba da haɗin kai wajen kare kayayyakin makarantar domin hana ɓata-gari lalata su.

Hakazalika a Makarantar Firamare ta Ringimawa kuwa, ya umarci shugaban makarantar da ya tabbatar an kula da sabbin bishiyoyin da aka dasa domin su girma yadda ya kamata.

Bugu da Kari,  a Makarantar Firamare ta Ciromawar Idi kuma, Malam Yusuf Kabir ya hori ɗan kwangilar da ya ƙara himma domin kammala aikin cikin wa’adin da aka tsara.

A dukkanin makarantun da ya ziyarta, Shugaban ya nuna gamsuwarsa da ingancin ayyukan da ake gudanarwa, tare da jaddada cewa Hukumar ba za ta amshi wani aiki da bai cika ƙa’idodin inganci ba.

Malam Yusuf Kabir ya yi amfani da wannan dama ya ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusif bisa jajircewasr wajen ganin ya inganta fanni Ilimi a jihar nan

Related Articles

Back to top button