MUNA MARHABUN DA DUK WATA GUDUMMAR TALLAFAWA ILIMI- SHUGABAN SUBEB

Daga Alhassan Hassan
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir ya bayyana cewa Hukumar tana marhabun da duk wata gudummawa da zata bunkasa hakar ilimi a jihar nan.
Malam Yusif Kabir ya furta hakan a lokacin da yake duba wasu sabbin bandakuna da Kungiyar Masu aikin gado ta Kwankwasiyya Gandun Albasa suka gina a Karamar Makarantar Sakandare ta Jigirya a yankin Karamar Hukumar Nasarawa.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mai rikon Daraktan sashen wayar da kai na Hukumar , Balarabe Danlami Jazuli ya nuna matukar farin cikinsa tare da godewa wannan kungiya bisa wannan abin alheri da suka yi wa makarantar.
Malam Yusif Kabir ya nanata cewa kungiyoyi da sauran al’umma na da muhimmiyar rawar takawa wajen tallafawa gwamnati a hakar samar da ilimi, bisa haka ne ya yi kira ga daukacin alumma su yi koyi da Kungiyar Masu aikin gado ta Kwankwasiyya Gandun Albasa, wajen kai gudummawa ga makarantu.

Tun da fari shugaban kungiyar Malam Nafiu Nuhu ya ce kungiyar bisa jagorancin wani maikishin alumma Alhaji Umar Idi suka binciki matsalar makarantar, inda suka himmatu wajen magancewa ta hanyar gina bandakuna da hada rijiyar Burtsatse a wani bangare na bayar da tasu gudummawar ga harkokin ilimi.
Malam Nafiu Nuhu ya kara jadda aniyar kungiyar wajen ci gaba da tallafawa kokarin gwamnatin Inijiniya Abba Kabir Yusif a hakar samar da ilimi tun daga tushe.




