LabaraiUncategorized

ziyarar shugaban AOPSHON

DAGA JB DANLAMI

Zan bar kafa ta a bude don karbar shawarwari – Sabon shugaban kungiyar Hedimastoci

Sabon Shugaban kungiyar shugabanin makarantun Firamare na jiha (AOPSHON) Malam Abdussalmu Sumaila, ya bayyana cewa zai bar kofarsa a bude don karbar shawarwarin daga membobin kungiyar don ci yar da harkokin kungiyar gaba.

Mallam Abdussalam, ya furta haka a lokacin wata ziyara da ya kai ofishin Hulda da Jama’a na Hukumar Ilimin Bai Daya dake sakatariyyar Audu Bako.

Ya kara da cewa, makasudin wannan ziyara ita ce don ya gabatar da kansa a matsayinsa na sabon shugaba Kungiyar tare da neman gudummawar sashen na yada labarai wajen sanar da alumma aikace aikacen kungiyar.

Shugaban ya yi amfani da wannan dama, ya ja hankalin shugabannin makarantu kan jajircewa a ayyukansu a matsayinsu na shugabannin matakin farko a tsarin shugabancin harkokin ilimi.

“Kungiyoyinmu suna kare mutuncin ‘ya yansu, idan aka yi niyar cin zarafinsu, amma idan dan kungiya ya aikata rashin gaskiya to ba mu da hurumin kare shi” in ji sabon shugaban

Kazalika, mallam Abdussalamu ya taya shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya murnar Samun lambar yabo daga Maaikatar Ilimi ta tarayya, sai kara da cewa wannan lambar yabo ta zama abun alfari ga daukacin alummar jihar nan baki daya.

A lokacin wannan wannan ziyarar Sabon Shugaban kungiyar shugabanin makarantun Firamare na jiha (AOPSHON) Malam Abdussalmu Sumaila yana tare da sabuwar sakatariyar kungiyar ta jiha, Malama Bilkisu T. ABdulkadir

Related Articles

Back to top button