EducationUncategorized

 KH Gaya ta kaddamar da daukar Sabbin Dalibai na Shekarar Karatu ta 2025/2026

 KH Gaya ta kaddamar da daukar Sabbin Dalibai na Shekarar Karatu ta 2025/2026

Daga JB Danlami

Karamar Hukumar Gaya ta kaddamar daukar sabbin dalibai na firamare na shekarar karatu ta 2025/2026, wanda aka gudanar a makarantar firamare ta Gaya Kofar Fada cikin birnin Gaya.

A jawabinsa, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusuf Kabir, wanda Daraktan Sashen Wayar da Kai, Malam Balarabe Danlami Jazuli, ya wakilta, ya bayyana muhimmancin gudanar da  taron daukar sabbin dalibai, yana mai jaddada cewa wannan aiki na daga cikin muhimman matakai da ke tabbatar da kowa ya samu damar samun  ilimi tun daga tushe.

A nasa bangaren, jami’in UBEC na Jihar Kano, Malam Abdurrahman Musa, ya bayyana cewa Hukumar UBEC tana bai wa fannin wayar da kan al’umma muhimmanci sosai, domin tabbatar da cewa iyaye suna ba da fifiko ga ilimin ‘ya’yansu a kowane mataki.

Da yake jawabi Kansilan Ilimi na Gaya, Hon. Abdullahi Muhammad, wanda ya wakilci shugaban karamar hukumar, ta Gaya Hon. Tajo Muhammad Sani Gaya, ya yi tsokaci mai tsawo kan irin muhimmancin da Karamar Hukumar ke bai wa bangaren ilimi. Ya bayyana cewa an samar da babura da mota domin inganta fannin duba makarantu, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da ingantacciyar kula da al’amuran ilimi a yankin.

A ƙarshe, Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Gaya, Malam Suraja Akilu, ya gabatar da jawabin godiya, inda ya gode wa dukkan mahalarta da suka bayar da gudunmawa wajen tabbatar da nasarar gudanar da wannan biki na musamman

Related Articles

Back to top button