Labarai

Wata kungiya ta karrama Mai rikon shugabancin Hukumar Ilimin Bai Daya

 

Daga JB Danlami

Wata kungiya wadda a turance ake kira da Trusted Northern Youth awareness ta karrama mai rikon shugabancin Hukumar Ilimin Bai daya Hajiya Amina Umar da lambar Girmaamawa.

Da ya mika takardar ga mai rikon shugancin Hukumar a ofishinta, shugaban Kungiyar Malam Sani Ibrahim ya ce manufar karramawar ita ce don karfafa guiwar jami’ai da suke da halayyar jajircewa a bakin aiki.

Ya kara da cewa Hajiya Amina ta cancanci wannan karramawa bisa la’akari da yadda take gudanar da aiki bisa nuna jajircewa a matsayinta na darktar sashen zaburawa wadda a yanzu take rike shugabancin Hukumar.

Da take jawabin godiya, mai rikon shugabancin Hukumar Ilimin Bai daya, Hajiya Amina Umar, ta bayyana wannan karramawa da cewa ba ita kadai aka yiwa ba, har da daukacin ma’aikatan sashen zaburarwa da ma sauran ma’aikatan hukumar ba ki daya, inda ta yi alwashin ci gaba da hulda da kungiyar a yunkurinsu wajen tallafawa harkokin alumma.

Da yake jawabi tun da fari, mai rikon Daraktan sashe zaburarwar na hukumar Malam Balarabe Danlami Jazuli, ya bayyana cewa sashen na aiki da kungiyoyi na cikin gida da kasashen waje don bunkasa shigar alumma cikin harkokin bunkasa ilimi.

Related Articles

One Comment

Back to top button