An yabawa Shugabannin makarantu na yankin KH Takai bisa nuna kwazo wurin aiki
Shugabannin makarantu na yankin KH Takai bisa nuna kwazo wurin aiki

Daga TAKAI LGEA
Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Takai, Malam Abdullahi muhd Yusuf ya yabawa shugabannin makarantun bisa jajircewarsu kan ayyukansu.
Malam Abdullahi ya yi a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin makarantun firamare da na Kananan Makarantun Sakandare dake yankin
Sakataren Ilimin ya ci gaba da cewa makasudin taron shibne zaburar da shugabanin makarantun don gudanar ayyukansu, daidai gwargwado.
ya kira da yin aiki kafada da kafada da kungiyoyin da suke da nasaba da makarantunsu, kamar Kwamitocin Alumma gatan makaranta ( SBMC) da Kungiyar iyaye da Malaman Makaranta( PTA,) da Kungiyar Iyaye Mata ( MOTHER’S ASSOCIATION,) da Kungiyoyin Tsoffin Dalibai (OPA) da masu bayar da tallafi na cikin gida da na wake (DONORS) inda ya Kara da cewa muamalla da su zasu tallafa wa makarantu da abubuwa da dama wajen ingantuwar ilimi a wannan karamar hukuma.




