An gudanar da taron bita ga Kwamitocin SBMC a KH Shanono
An gudanar da taron bita ga Kwamitocin SBMC a KH Shanono

Daga Shehu Garba
Shanono LGEA
Sashe zaburarwa da fadakar da alumma na yankin Karamar Hukumar Shanono sun gudanar da taron taron horarwa ga sabbin Shugabannin Kwamitocin Alumma Hatan Makaranta (SBMC/
Da yake jawabi wajen bude taro Sakataren ilimi na yankin Malam Muntari Musa Shakogi ya ja hankalin sabbin shugabannin SBMC na yankin da su kara dagewa sauke nauyin da aka dora misu na jagorantar harkokin makarantu. Sannan ya nuna godiyarsa wajen samun damar halartar wannan taro.
Da yake jawabi kansilan Ilimi na yankin sunansa ,…., ya bukaci shugabannin shiga lungu da sako domin tabbatuwar koyo da koyarwa a wannan karamar hukumar.
Ya kara da cewa shugaban karamar hukuma a tsaye yake domin taimakon ma’aikatar da bada gudummawa domin inganta harkar koyo da koyarwa. Kazalika ya kara da cewa kasancewar wannan taro an dauko mutum 3 ne daga kowacce makaranta za’ a tabbatar da dukkan yan kungiyar alumma gatan makaranta sun sami wannan horo na sanin makamar aiki.
A karshe shugaban sashen zaburarwa da wayar da kai MALAM SHEHU GARBA ya tabbatar da bin makarantun lungu da sako na wannan karamar hukumar domin yin taro da kunshin shugabanci na mutane 17 na kowacce makaranta.
Shugaban Sashen zaburarwa SHANONO LGEA
SHEHU GARBA.




