Shugaban SUBEB ya taya malaman makaranta murnar bikin ranar malamai ta duniya
Shugaban SUBEB ya taya malaman makaranta murnar bikin ranar malamai ta duniya

Daga JB Danlami
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir, ya taya malaman makaranta murnar bikin Ranar Malamai ta Duniya, tare da yn kira gare su da su kara zage damtse wajen gudanar da ayyukansu na koyarwa
Wannan bayani na kunshe ne cikin wata sanarwa da Balarabe Danlami Jazuli, Daraktan sashen Wayar da Kai na Hukumar, ya sanya wa hannu.
Shugaban ya bayyana cewa wannan rana wata muhimmiyar dama ce ga malamai domin su duba matsalolin da suka fuskanta a baya, tare da nuna godiya ga ci gaban da aka samu musamman a zamanin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusif.
Malam Yusif ya jaddada cewa a cikin kankanin lokaci, Gwamnatin ta warware matsalolin karin girma (promotion) da malamai suka dade suna fama da su. Haka kuma, an inganta biyan kudaden alawus na jagoranci (duty allowance).
Haka zalika, ya bayyana cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusif ta kara daukar malaman makaranta, tare da fito da wani tsarin bayar da bashi mara ruwa ga malamai don inganta walwalarsu
Baya ga hakan, gwamnatin ta gina sabbin ajujuwa da gyara wasu da dama domin inganta walwalar malamai da dalibai.
A karshe, Malam Yusif Kabir ya bukaci malaman makaranta da su ci gaba da jajircewa a bakin aikinsu a matsayin nuna godiya ga gwamnatin bisa kokarinta na farfado da harkar ilimi a matakin farko.



