Labarai

MUN YI RASHIN HAZIKIN MA’AIKACI-IN JI SHUGABAN SUBEB

Daga JB Danlami

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na jiha, Malam Yusif Kabir ya mika sakon ta’aziiyarsa ga iyalan  marigayi Malam Abdullahi Tsoho Gwarzo.

Marigayi Malam Abdullahi, ya rasu a safiyar Alhamisdin nan sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyarsa ta zuwa wurin aiki.
Malam Yusif ya bayyana kaduwarsa matuka, bisa samun labarin rsuwar Malam Abdullahi Tsoso. inda ya kara da cewa Hukumar SUBEB zata ci ga ba tunawa da marigayin bisa sadaukar da kansa wajen hidimtawa harkar Ilimi a jihar nan.
Ya yi adduar Allah ya jikansa, ya bai wa iyalansa hakurin jure rashin.
Kafin rasuwarsa, Malam Abdullahi Tsoso Gwarzo ma’aikacin Hukumar Ilimin Bai Daya ne a shiyyar Ilimi ta Kiru

Related Articles

Back to top button