Labarai

Mun shirya tsaf don daukar bayanan ma’aikatanmu- Hajiya Amina

Daga JB Danlami

Mai rikon Shugabancin Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha, Hajiya Amina Umar ta ce Hukumar ta shirya gudanar da aikin kididdigar adadin Ma’aikata da suke aiki hedkwatar hukumar da shiyyoyi sha biyar da sassan Ilimi na kananan hukumomi arbain da hudu da suke a fadin jihar nan.

Mairikon Shugabancin Hukumar ta bayyana hakan ne a lokacin wani taro da daractocin hukumar.Hajiya Amina ta kara da cewa manufar aikin ita ce don daukar bayanan daukacin ma’aikatan hukumar a dukkan matakai da nufin sanin adadin Ma’aikata a kowanne sashe, kazalika da dora ma’aikatan a gurbin aiki da ya dace da fannin iliminsu da kuma kwarewarsu.

Har ila yau ta nanata cewa wannan zai kasance wani madubi da Hukumar zata yi aiki da shi wajen dora ma’aikata a gurbin aiki da zai taimaka wajen imganta ayyukan ci gaban ilimi a dukkan matakai.Mai rikon Shugabancin Hukumar ta hori daraktocin shiyyoyi da sakatarorin ilimi su tabbatar da cewa sun gabatar da bayanan ma’aikatansu don gudun kar a bar wani ko wata a baya.

Data juya ga ma’aikatan da al’amarin ya kuwa shugabar ta ja hankalin su da su tabbata sun halarci wurin daukar bayanan a duk lokacin da za’a gudanar da wannan aiki.

“ Duk wani ko wata da suka gaza hallara a wurin wannan aiki ba tare wani dalili mai karfi ba, wannan na nuni da cewa akwai ayar tamabaya kuma hakan na iya sawa a cire sunan wadanda suka ki zuwa wajen wannan aiki daga jerin halattun ma’aikata” jn Hajiya Amina

Ta yi amfani da wannan dama ta godewa kwamishinan ilimi,  Alhaji Umar Haruna Doguwa bisa sahalewa Hukumar ta gudanar wannan aikin.

Related Articles

Back to top button