Labarai

Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha ta fara Gudanar da taron bita ga Malaman Makarantun Model

Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha ta fara Gudanar da taron bita ga Malaman Makarantun Model

Daga JB Danlami

A wani sabon yunƙuri na inganta ingancin koyarwa da koyo a matakin ilimi na farko, Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB) ta fara gudanar taron bita musamman ga malaman makarantun Misali (Model School)

Shugaban Hukumar SUBEB, Malam Yusuf Kabir, ya sanar da haka ta bakin Daraktar horar da malamai Hajiya Hauwa Tanimu, a lokacin bude taron bitar da yake gudanar
a Cibiyar horar da malamai da ke Kwalejin Sa’adatu Rimi, Kumbotso.

Hajiya Hauwa ta bayyana cewa horon wani bangare ne na ci gaba da kokarin hukumar wajen haɓaka ƙwarewar malamai ta hanyar koyar da su dabarun tsara darasi da kuma isar da shi cikin inganci.

A cewarta, manufar taron bitar ita ce koyar da malamai dabarun lura da aji, koyar da karatu da lissafi, tare da inganta hanyar koyarwa a makarantun.

Ta ƙara da cewa, Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta dauki nauyin taron bitar don horadda malaman makarantun model da aka zabo daga makarantun model 100 daga Kananan Hukumomi 25 a faɗin jihar.

Daraktar ta bayyana cewa horon zai ɗauki kwana biyar, kuma za a koyar da mahalarta dabaru da ƙwarewar da za su inganta gudanar da darasi da kuma haɓaka sakamakon karatu na ɗalibai.

Hajiya Hauwa Tanimu ta jaddada cewa burin wannan horo shi ne ba kawai a inganta ƙwarewar koyarwa na malamai ba, har ma da haɓaka sakamakon koyo na ɗaliban makarantun gwamnati.

Ta yaba da jajircewar mahalarta horon, tare da buƙatar su yada ilimin da suka samu ga sauran abokan aikinsu domin samun gagarumin tasiri a sauran makarantun.

A madadin Shugaban Hukumar, Hajiya Hauwa Tanimu ta godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa sadaukarwarsa da kuma ɗaukar tsare-tsare masu amfani da ke haɓaka harkar ilimi a jihar.

Related Articles

Back to top button