Education

An yaba wa Shugabannin Kananan Makarantun Sakandare na KH Gwale bisa jajircewa wurin ayyukansu

An yaba wa Shugabannin Kananan Makarantun Sakandare na KH Gwale bisa jajircewa wurin ayyukan

By JB Danlami

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir, Ya Yaba da Jajircewar Shugabannin Kananan Makarantun Sakandare na Karamar Hukumar Gwale

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jihar Kano, Malam Yusif Kabir, ya yaba da yadda shugabannin kananan makarantun sakandare na Karamar Hukumar Gwale ke jajircewa wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Malam Yusif Kabir ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga shugabannin makarantun a wajen wani taro da suka gudanar a Makarantar Firamare ta Gadan Kaya, da ke yankin Karamar Hukumar Gwale.

A cikin jawabin nasa, shugaban ya bukaci shugabannin makarantun da su hada hannu da kwamitocin SBMC (School-Based Management Committee), da kungiyoyin PTA (Parents Teachers Association), da kuma ƙungiyoyin tsoffin dalibai domin samar sabbin hanyoyin aiwatar da ayyuka da za su inganta harkar ilimi a makarantunsu.

Kazalika, ya bukaci shugabannin da su kara zage damtse wajen samar da tsare-tsare na inganta tsaro da za su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin makarantun.

Har ila yau, Malam Yusif Kabir ya yi amfani da wannan dama wajen yin godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa daukar sabbin malamai da amincewa a tura su zuwa makarantun firamare da kananan sakandare, domin bunkasa harkokin ilimi a jiha

Related Articles

Back to top button