Sashen Ilimin KH Ungogo ya shirya taron adduoi a makarantun yankin
Sashen Ilimin KH Ungogo shirya taron adduoi a makarantun yankin

Daga JB Danlami
Sakatariyar Ilimin Karamar Hukumar Ungogo, Hajiya Hussaina Ibrahim, ta bayyana muhimmancin addu’a a matsayin babbar kariya daga duk wani kalubale da ka iya zama barazana ga ci gaban al’umma. Ta yi wannan jawabi ne yayin karin haske kan tarukan addu’o’in da aka gudanar a makarantun firamare da kananan sakandare na yankin.

Ta ce taron ya biyo bayan umarnin da suka samu daga Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB), Malam Yusuf Kabir, inda ya umurci makarantun da su hada kan dalibai da malamai domin gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da karin arziki ga jihar Kano da kasa baki daya.
Hajiya Hussaina ta bayyana cewa Kano na ci gaba a fannoni da dama sakamakon zaman lafiya da Allah Ya albarkace ta da shi, sai dai a wasu yankuna ana fuskantar kalubalen tsaro da ke haifar da fargaba ga mazauna wuraren.

Ta kara da cewa an gudanar da addu’o’i na musamman domin neman kariyar Allah ga Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf da daukacin al’umma daga duk wani sharri ko barna.
Bugu da kari, Sakatariyar ta yi godiya ga Kungiyar Malamai (NUT), Kungiyar Hejimastoci (AoPSHON), da Kungiyar Ma’aikata (NASU) bisa cikakken goyon bayan da suka bayar wajen samun nasarar gudanar da taron adduar

Taron adduoin ya kunshi Sallar nafila da wa’azi da yin zikiri.



