Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha Ya Mika Sakon Ta’aziyya Bisa Rasuwa Matasa 22 a Hatsarin Mota
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha Ya Mika Sakon Ta’aziyya Bisa Rasuwa Matasa 22 a Hatsarin Mota

Daga JB Danlami
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir, ya mika sakon ta’aziyya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, bisa rasuwar matasa 22 ‘yan asalin jihar nan da suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota.
Hatsarin, wanda ya afku ne yayin da matasan ke dawowa daga gasar wasannin kasa da aka gudanar a Jihar Ogun, ya jefa al’ummar jihar cikin jimami da alhini.
Malam Yusif Kabir, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa wannan babban rashi ne ba ga iyalan marigayan kadai ba, har da gwamnatin jiha da daukacin al’ummar Kano baki daya.
Ya kuma mika irin wannan sakon ta’aziyya ga Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, da iyalan marigayan da sauran al’umma.
Ya bayyana cewa: “Wannan hatsari babbar jarrabawa ce da ta girgiza mu gaba ɗaya. Muna rokon Allah Ya gafarta wa matasan da suka riga mu gidan gaskiya, Ya kuma ba wa iyalansu da abokansu hakurin jure wannan rashin.”
Kazalika, shugaban hukumar ya yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata a hadarin, yana mai kira ga Dalibai da malaman Makarantaun firamare da kananan Makarantun sakadare da su ci gaba da yin addu’o’i don neman kariya daga irin wannan jarrabawa.
A ƙarshe, Malam Yusif ya bukaci daukacin da su ci gaba da jajircewa wajen nuna damuwa da tallafa wa juna, musamman a lokutan jarrabawa irin wannan.




