Labarai

KUNGIYAR MALAMAN BESDA TA JIHA SUN  ZIYARCI  HEDIKWATAR HUKUMAR ILIMIN BAI DAYA

DAGA JB DANLAMI

kungiyar malaman BESDA ta jiha, sun bayyana hajiya amina umar a matsayin hazikar ma’aikaciya.

Mataimakin shugaban kungiyar na jiha, kuma wanda shi ne shugaban kungiyar a Karamar Hukumar Birni, Aminu Bala Sanda ya jagoranci ayarin Malaman BESDA zuwa  wata ziyara da suka kawo  Hedikwatar Hukumar Ilimin Bai Daya dake sakatariyyar Audu Kabo.

Aminu Bala Sanda ya ce, sun ziyarci hukumar ce don su nuna godiya ga Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusif bisa lamuncewarsa aka  biya  su kudaden alawusdinsu na watanni a lokaci guda.

Ya kara da cewa, ziyar ta su ta hada da taya murna ga sabon Shugaba da aka nadawa Hukumar, wato Malam Yusif Kabir kazalika, da yi wa tsohuwar mai rikon Shugabancin Hukumar Hajiya Amina Umar fatan alheri na rike mukamin da ta yi kuma ta cimma nasarori da dama.

Muna rokon sabon Shugaban Hukumar ya yi mana irin rikon da mamar Hajiya Amina ta yi mana, inda ako da yaushe take sauraron kukanmu tare da share mana hawaye” in ji Mataimakin shugaban kungiyar

Da take mayar da jawabi, tsohuwar mai rikon Shugabancin Hukumar, Hajiya Amina Umar ta godewa Malaman BESDA  bisa yadda suke bayar da gudummawa at fuskar koyar da dalibai  da kuma yadda suke nuna godiya ga yadda gwamnati take bakin kokari wajen warware musu duk wasu matsaloli, inda ta kara da cewa sabon shugaban Hukumar Malam Yusif Kabir goggen ma’aikaci ne da zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin an ci gaba da amfanuwa da gudummawar da suke bayarwa ta fuskar habaka harkar ilimi a jihar nan.

Ana nasa jawabin mai rikon Daraktan wayar da kai, Balarabe Danlami Jazuli ya nusar da malaman cewa harkar ilimi na bukatar gudummawa daga kowa da kowa, don  haka akwai bukatar su ci gaba da marawa kokarin gwamnati wajen ganin an kawar da jahilci a tsakanin alumma.

A lokacin wannan ziyara Malaman BESDA sun mika kyautar girmamawa ga tsohuwar mai rikon Shugabancin Hukumar Hajiya Amina Umar.

Related Articles

Back to top button