Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha ta shirya taron Wayar da kan alumma a Karamar Hukumar Warawa
Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha ta shirya taron Wayar da kan alumma a Karamar Hukumar Warawa

Daga Jb Danlami
Hukumar limin Bai Daya ta Jihar Kano ta shirya taron wayar da kai a Karamar Hukumar Warawa, domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan matsalolin da suka shafi karatun yara, tare da lalubo hanyoyin magance su.

Taron, wanda ya gudana bisa umarnin Shugaban Hukumar, Malam Yusif Kabir, ya samu halartar jami’an ilimi, shugabannin makarantu, wakilan al’umma, da sauran masu ruwa da tsaki.
A yayin taron, Daraktan Sashen Wayar da Kai na hukumar, Balarabe Danlami Jazuli, wanda ya samu wakilcin Mukaddashiyar Darakta, Hajiya Aisha Shuaibu, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin magance matsalolin rashin zuwa makaranta da yara ke fuskanta a yankin.

Ya bayyana cewa rahoton da Sashen Bibiyar Ayyukan Makarantu ya fitar ya nuna cewa yara da dama ba sa halartar makaranta yadda ya kamata a wasu makarantu da ke yankunan Imawa, Jigawa, da Token.
“Taron masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen fahimtar tushen matsalolin da kuma daukar matakan da suka dace don inganta halin da ake ciki,” in ji shi.
Daraktan ya jinjinawa Gwamnan Jihar Kano, Malam Abba Kabir Yusif, bisa irin goyon bayan da yake bai wa Hukumar Ilimin Bai Daya. Ya ce wannan tallafi ya ba Shugaban Hukumar, Malam Yusif Kabir, damar bullo da sabbin tsare-tsare masu inganta ilimi a jihar.
Shugaban Karamar Hukumar Warawa, Hon. Lamido Sunusi Ahmad, wanda ya samu wakilcin Mai ba shi shawara kan harkar ilimi, Hon. Mustafa Yakubu Ado, ya bayyana cewa ana shirin kafa Kwalejin Horar da Malamai a yankin domin samar da malamai ‘yan asalin yankin da za su shiga lungu da sako don koyar da dalibai.

Bugu da kari, ya bayyana cewa ana kokarin gina sabbin ajujuwa, samar da kayan aikin makarantu, da bunkasa fannin ilimi a yankin gaba daya.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Al’umma Gatan Makaranta na Jiha, Malam Tijjani Haladu Baraya, wanda mataimakinsa Alhaji Garba Adamu ya wakilta, ya ce wannan taro ya zo a daidai lokacin da kwamitin ke kokarin tallafawa gwamnatin jihar wajen samar da ilimi mai inganci ga yara.
Haka nan, Sakataren Ilimin yankin, Malam Muhammad Sani Ishak, ya bayyana cewa an kammala shirye-shiryen wayar da kai a yankuna daban-daban na Karamar Hukumar Warawa, domin ilmantar da iyaye game da mahimmancin sanya ‘ya’yansu a makaranta da kuma kula da halin da suke ciki har zuwa kammala karatunsu.
Dagacin Kanta, Salisu Abdu Ciranci, ya ja hankalin shugabannin al’umma da su hada hannu da gwamnati wajen wayar da kan iyaye, domin tabbatar da cewa yara na zuwa makaranta ba tare da tangarda ba.

Taron ya bai wa mahalarta damar tattaunawa kan matsalolin da ke hana yara halartar makaranta, tare da samar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi don inganta karatun yara a yankin.
Mahalarta sun yaba da kokarin Hukumar Ilimin Bai Daya tare da yin kira ga gwamnati da sauran kungiyoyin da ke bada gudunmawa a bangaren ilimi da su ci gaba da tallafawa wannan yunkuri.
Taron ya samu halartar shugabannin makarantu, Shugaban CRC na yankin, wakilan kungiyoyin al’umma, da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.



