Muna yabawa da tsare-tsaren inganta Ilimi da Gwamnati ta bullo da su

Daga JB Danlami
Shugaban Kungiyar Shugabanin makarantun firamare jiha, kwamarad Malam Abdussalam ya yabawa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa matakai da gwamnatinsa take dauka na inganta fannin ilimi a jihar nan.
Malam Abdussalamu, ya bayyana hakan ne, da yake jawabi bayan kammala aiki duba makarnatu a yankin Karamar Hukumar Sumaila, wanda shugaban hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha Malam Yusuf Kabir ya jagoranta.
Shugaban Kungiyar ya ci gaba da cewa, sabon tsarin duba makarantu da shugaban Hukumar ta Ilimin Bai Daya ya bullo da shi, inda yake jagorantar daukacin jami’an Hukumar, don kai ziyara a makarantu a karamar Hukumar guda da cewa hakan zai taimaka wajen lalubo matsaloli ilimi don daukar matakan da suka kamata.
Malam Abdussalam, ya godewa hukumar bisa gudanar da taron tattaunawa da shugabanin makarantu don ji daga bakinsu, ire-iren matsaloli da suke hana ruwa gudu ga ci gaban ilimi don hada hannu da nufin magance su.
Ya kuma yi amfani da wannan dama, ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa yadda yake gina sabbin ajujuwa da gyaran wasu da dama da samar da kayan aiki a makarantu da inganta walwalar malamai da makamantansu.
Har ila yau, shugaban kungiyar Shugabannin makarantu firamaren, ya nuna jin dadinsa bisa yadda hukumar take iya kokairn sanyawa shugabannnin makarantu alawus na shugabanci don kara musu kwarin guiwa wajen gudanar da ayyukansu.




