LabaraiUncategorized

Ya zama wajibi a bi ka’ida wajen nadin Shugabanin makarantu- Shugaban SUBEB

Daga JB Danlami

A wani mataki da Hukumar ilimi Bai daya ta jiha ta dauka don samar da ingantacce tsarin shugabanci a Makarantu firamare da kananan makarantun Sakandare, Shugaban Hukumar Malam Yusif Kabir ya sanar da sabin kaidojin nada shugabanin Kananan makarantun sakandare da na firamare da kuma mataimakansu.
Malam Yusif Kabir, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ta fito daga mai riko sashen wayar da kai na hukumar Balarabe Danlami Jazuli wadda aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, ya zama wajibi duk wadanda za’a nada a mukamin shugaban karamar makarantar sakaradare, ya zama yana kan matakin albashi na sha uku kuma ya kasance ya yi aiki na tsawon shekaru sha biyar ko fiye, inda mai taimaka masa zai kasance a matakin albashi na sha biyu, kazalika wadanda za’a nada su kasance suna da matakin ilimi na digiri ko sama da haka. Bugu da kari ana bukatar su da kwarewa kan Magana da turanci ko larabci. Har ila yau, ana bukatar yin la’akari da nada mata su shugabanci makarantar mata inda shugabanin maza kuma zasu shugabanci makarantar maza zalla

Sai kuma ka’idar nadin shugaban makaratar firamare, ina ya zama wajibi duk wadanda za’a nada a mukamin shugaban, ya zama yana kan matakin albashi na sha biyu, inda shugaban makarantun ‘ya ‘yan makiya zai kasance a matakin albashi na goma kuma ya kasance sun yi aiki na tsawon shekaru sha biyar ko fiye, inda mai taimaka wa shugabanin makarantun firamare zasu kasance a matakin albashi na sha biyu, kazalika wadanda za’a nada su kasance suna da matakin ilimi na shaidar ilimi ta kasa (NCE) ko sama da haka. Bugu da kari ana bukatar su da kwarewa kan Magana da turanci ko larabci ko fillanci ga makarantu ‘ya yan makiyaya, ya kuma zama wajibi ga duk wadanda aka zaba su shugabanci makarantu ‘ya yan makiyaya su kasance masu dabiu da suka danganci na fulani . Har ila yau, ana bukatar yin la’akari da nada mata su shugabanci makarantar mata, inda shugabanin maza kuma zasu shugabanci makarantar maza zalla.

Malam Yusif Kabir ya hori sakatarorin ilimi su tabbata sun yi amfani da wadan nan kaidoji da nufin ganin an kara tsarin shugabanci a makarantu da su karkashin hukumar.

Kazalika ya godewa gwamna Abba Kabir Yusif bisa yadda yake bayar da kulawar da takamata ga fannin ilimi a jihar nan

 

Related Articles

One Comment

Back to top button