Labarai

Muna marhabun da duk wani Shiri da zai tallafawa Ilimi – Shugaban SUBEB

Mun marhabun da duk wani Shiri da tallafawa Ilimi - Shugaban SUBEB

Dag JB Danlami

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jihar Kano, Malam Yusuf Kabir, ya yabawa Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Birni, Hon. Sagir Ibrahim Koki, bisa jajircewarsa wajen tallafawa harkar ilimi a yankinsa.

Wannan yabo ya fito ne yayin bikin raba kayan makaranta ga dalibai 622 na Karamar Sakandire Laure wadda da Dan majalisar ya gyara a unguwar Koki, cikin Karamar Hukumar Birni.

A jawabinsa, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya Malam Yusuf Kabir, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Ilimi na Daya, Hon. Wada Ibrahim Daho, ya bayyana cewa wannan aiki na Hon. Sagir Ibrahim Koki yana nuna kishinsa da kokarinsa wajen bunkasa ilimi a yankinsa. Ya kara da cewa hadin gwiwa daga kowane bangare na al’umma yana da matukar muhimmanci don inganta harkar ilimi.

Shugaban Karamar Hukumar Birni, Hon. Salim Hashim Gwangwazo, ya jinjina wa Hon. Sagir Koki bisa wannan namijin kokari, tare da yin kira ga daliban da suka amfana da su yi amfani da kayan yadda ya dace domin amfanin iliminsu.

A nasa bangaren, Hon. Sagir Ibrahim Koki ya bayyana cewa wannan tallafi da ya yi kan ilimi somin tabi ne. Ya kara da cewa nan ba da dadewa ba za a zabi makaranta daya a kowacce daga cikin mazabu 13 na Karamar Hukumar Birni domin samar da kwamfuta da inganta ilimin fasaha a yankin.

Daya daga cikin daliban da suka amfana, Nura Tijjani, ya godewa dan majalisar a madadin dalibai, tare da yin alkawarin amfani da kayan da aka basu yadda ya kamata don ci gaban iliminsu.

Kayan da aka raba sun hada jakunkuna da littattafi da takarma da sauransu

Kazalika Dan majalisar tarayya ya gyara ajujuwa sha shida da bandakuna sha shida da ofisoshin malamai

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button