Labarai

SBMC da PTA na Makarantar Sakandaren Arabiya Ta Mata dake Kachako Sun Ziyarci Sakataren Ilimi na Takai

SBMC da PTA na Makarantar Sakandaren Arabiya Ta Mata dake Kachako Sun Ziyarci Sakataren Ilimi na Takai

Daga Nura Rabiu Takai

Kwamitin Alumma gatan Makaranta (SBMC) tare da Kungiyar Iyaye da Malamai (PTA) na Makarantar Sakandaren Arabiya Ta Mata da ke garin Kachako sun kai ziyara ga Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Takai, Malam Abdullahi Muhammad Yusuf, a ofishinsa.

A yayin karɓar ayarin, Sakataren Ilimin ya bayyana jin daɗinsa bisa wannan ziyara, inda ya sha alwashin daukar matakan da suka dace domin magance wasu muhimman matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban ilimi a makarantar. Matsalolin sun haɗa da karancin malamai da kuma rashin masu gadi.

Malam Abdullahi Muhammad Yusuf ya jaddada cewa wannan ziyara ta zo a kan lokaci, tare da tabbatar da cewa Sashen Ilimi na Karamar Hukumar Takai zai duba koken da aka gabatar tare da daukar matakan da suka dace domin inganta harkokin koyarwa da tsaro a makarantar.

A nata jawabin, Shugabar Sashen Zaburarwa (Social Mobilization), Hajiya Halima B. Shehu, ta bayyana cewa ziyara irin wannan na da matukar muhimmanci, inda ta bukaci wakilan SBMC da PTA da su kara azama wajen lalibo hanyoyin tallafawa makarantu domin bunkasa ilimi tun daga tushe.

Tun da fari, Mai magana da yawun ayarin, Malam Ado Tukur Kachako, wanda shi ne Shugaban PTA na makarantar, ya ce sun kai ziyarar ce domin sanar da Sakataren Ilimin wasu kalubale da makarantar ke fuskanta, musamman karancin malamai da rashin masu gadi, tare da neman tallafi wajen magance su.

Wakilinmu na sashen Sashen sadarwa a Karamar Hukumar Takai Malam Nura Rabiu Takai, ya bayyana cewa kungiyoyin biyu sun nuna farin ciki bisa kyakkyawar tarba da aka yi musu, tare da nuna godiya ga jajircewar Sashen Ilimi wajen sauraron koken-Kokensu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button