Labarai

Shirin Tallafi na Hajaiya Rabi sun  Raba Kayan Makaranta Ga Yara Masu Bukata Ta Musamman a Fagge

Shirin Tallafi na Hajaiya Rabi sun  Raba Kayan Makaranta Ga Yara Masu Bukata Ta Musamman a Fagge

Daga Kabiru Fagge

Shirin Tallafi  na Hajiya Rabi Foundation Wata ta hannun Hajiya Ummi Alhassan, sun  raba kayan makaranta ga dalibai masu bukata ta musamman a Makarantar Gobirawa da ke Karamar Hukumar Fagge, domin tallafa musu wajen samun damar karatu cikin sauki da kwarin gwiwa.

Kayan sun kunshi jakunkunan makaranta, littattafai da sauran muhimman kayayyakin karatu, wanda aka gudanar karkashin Haj Rabi Foundation.

Da take jawabi a wajen taron, Hajiya Ummi Alhassan ta bayyana cewa makasudin wannan tallafi shi ne taimaka wa yara masu bukata ta musamman su samu daidaito da sauran dalibai, tare da rage wa iyayensu nauyin kashe kudade kan kayan makaranta.

“Mun gudanar da wannan rabon ne domin karfafa gwiwar yaran da ke da bukata ta musamman, tare da tabbatar da cewa rashin kayan makaranta ba zai zama dalilin da zai hana su cimma burinsu na ilimi ba.” Ta ce

Hajiya Ummi Alhassan ta kara da cewa tallafinta ya samo asali ne daga imaninta cewa ilimi ginshikin ci gaban al’umma ne, kuma duk yaro—ba tare da la’akari da halin da yake ciki ba—yana da ‘yancin samun ilimi mai inganci.

Ta kuma bukaci sauran masu hannu da shuni da kungiyoyi su kara ba da gudummawa wajen tallafa wa yara masu bukata ta musamman, domin su zama mutane masu anfani ga kansu da al’umma gaba daya.

A nasu jawaban, iyaye da malamai sun yaba da wannan namijin kokari, inda suka bayyana cewa tallafin zai taimaka matuka wajen rage matsalolin da daliban ke fuskanta a makaranta.

A yayin taron, Mai Girma Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Fagge, Malam Ibrahim Sallau, ya yabawa Hajiya Ummi Alhassan bisa wannan aiki na alheri, yana mai jaddada cewa irin wadannan ayyuka na tallafi suna taimakawa wajen karfafa tsarin ilimi, musamman ga yara masu bukata ta musamman.

Malam Ibrahim Sallau ya kuma karrama  Hajiya Ummi Alhassan da lambar yabo bisa gudummawar da take bayarwa ga ci gaban ilimi da walwalar al’umma a Karamar Hukumar Fagge.

A karshe, ya yi addu’ar Allah Ya saka mata da alheri, Ya kara mata lafiya da yalwar arziki, tare da tabbatar da cewa hukumomin ilimi za su ci gaba da maraba da duk wani shiri da ke inganta rayuwar dalibai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button