Labarai

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir, ya halarci bikin Ranar Malamai ta Duniya

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir, ya halarci bikin Ranar Malamai ta Duniya

Daga JB Danlami

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir, ya halarci bikin Ranar Malamai ta Duniya

Taron, wanda Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT) reshen jiha ta shirya, ya gudana ne a babban ofishin kungiyar da ke Gyadi-Gyadi, cikin Karamar Hukumar Tarauni.

A jawabinsa, Shugaban Hukumar ya yaba wa kungiyar bisa hadin kan da suke bayarwa ga Hukumar wajen horar da malamai da sauran ayyuka masu alaka da ci gaban ilimi.

Malam Yusif Kabir ya kara da cewa Gwamnatin Jiha tana bai wa sha’anin jin dadin malamai muhimmanci, musamman ta fuskar biyan albashi akan lokaci da aiwatar da karin girma (promotion).

Haka kuma ya bayyana cewa Gwamnati ta gina sabbin ajujuwa da ta gyara wasu da dama tare da samar da kayan aiki domin inganta yanayin koyarwa da koyo.

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa reshen jiha, Comrade Baffa Ibrahim Garko, ya yaba wa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif bisa kokarinsa na inganta walwalar malamai da yanayin aikinsu.

Ya ce: “Mun gode wa Gwamna bisa daukar sabbin malamai, gina karin ajujuwa, da kuma bayar da horo don kara sanin makamar aiki.”

Comrade Baffa ya kuma bukaci Gwamna da ya sanya wakili daga cikin mambobin kungiyar NUT cikin kwamitin fansho na jiha, domin magance matsalolin da malamai ke fuskanta a lokacin ritaya daga aiki

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button