Education

Sakatarorin Ilimi na Kananan Hukumomin Shanono da Tsanyawa Sun Yaba da Nasarar Gudanar da Jarrabawar Daukar Malamai a Bichi

Sakatarorin Ilimi na Kananan Hukumomin Shanono da Tsanyawa Sun Yaba da Nasarar Gudanar da Jarrabawar Daukar Malamai a Bichi

Daga JB Danlami

Sakatarorin Ilimin Kananan Hukumomin Shanono da Tsanyawa, Kwamarad Sule Alhaji Haruna da Kwamarad Hamza Hassan, sun yaba da yadda aka gudanar da jarrabawar daukar Malamai cikin tsanaki, gaskiya da kuma bin ka’idoji a cibiyar daukar jarrabawar da ke Kwalejin Ilimi ta Garin Bichi.

Sakatarorin Ilimin sun bayyana hakan ne jim kadan bayan masu neman aikin koyarwa daga kananan hukumominsu suka kammala rubuta jarrabawar a cibiyar, inda suka nuna gamsuwarsu da tsari da kuma kulawar da aka tanada domin tabbatar da adalci da ingancin jarrabawar.

Kwamarad Sule Alhaji Haruna da Kwamarad Hamza Hassan sun ce, duk da cewa a baya an fuskanci wasu kalubale da suka kai ga dage jarrabawar a wasu cibiyoyi, amma matakan da Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha ta dauka sun haifar da kyakkyawan sakamako. Sun jaddada cewa ingantaccen shiri, kulawa da sa ido sun taimaka wajen kawar da matsalolin da aka ci karo da su a baya.

Sun bayyana matukar godiyarsu ga Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha (SUBEB), Malam Yusuf Kabir, bisa jajircewarsa da tsayuwar daka wajen ganin an samar da sahihin tsari da ya tabbatar da gudanar da jarrabawar cikin nasara, tare da kare mutunci da darajar aikin koyarwa.

A cewarsu, wannan nasara ta samo asali ne daga kudurin Gwamnatin Jihar Kano na inganta ilimi a kowane mataki, inda ta dauki ilimi a matsayin ginshikin ci gaba. Gwamnatin Jiha, ta hannun Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha (SUBEB), ta ci gaba da aiwatar da manyan gyare-gyare da suka hada da daukar sabbin Malamai, horaswa da bunkasa kwarewar Malamai, inganta tsarin daukar aiki, da samar da ingantattun kayan koyarwa da muhallin koyo a makarantun firamare da na matakin farko.

Sun kara da cewa daukar Malamai ta wannan tsari na gaskiya da adalci na daga cikin dabarun Gwamnatin Jiha na magance karancin Malamai da kuma tabbatar da cewa dalibai suna koyon darussa daga kwararrun Malamai masu kwarewa da jajircewa.

Haka kuma, Sakatarorin Ilimin sun yi amfani da wannan dama wajen gode wa Shugabannin Kananan Hukumomin Shanono da Tsanyawa bisa cikakken goyon baya da hadin kai da suka nuna, musamman wajen jagorantar ‘ya’yansu da kuma samar da yanayi mai kyau da ya ba da damar rubuta jarrabawar cikin kwanciyar hankali.

Sun bayyana fatan cewa kokarin Gwamnatin Jiha da Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha na inganta ilimi zai ci gaba da dorewa, tare da kara habaka tsarin daukar Malamai a fadin jihar, domin samar da sahihin ilimi da zai amfanar da al’umma baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button