Labarai

Sashen Ilimi Karamar Hukumar Kura ya shirya taron adduoi a makarantun yankin

Sashen Ilimi Karamar Hukumar Kura ya shirya taron adduoi a makarantun yankin

JB Danlami

A Wani bagare na tarurrukan kammala Zangon karatu na farko na Shekarar 2015/2026 Karamar Hukumar Kura ta gudanar taron ranar Dalibai musulmi

Taron ya taron ya gudana a daukacin makarantu 159 wadanda suka hadar da makarantun firamare da kananun makarantun Sakandare da makarantun Islamiyya da na ‘ya ‘yan makiya.

Da yake jawabi ga Sashen yada labarai na Hukumar Ilimin Bai Daya, Sakataren Ilimin yankin Malam Aminu Alasan Karfi Sashen Ilimin ya umarci daukacin Makarantun su gudanar da Sallar nafila da adduoi tare da gudanar wa’azi domin nemawa jihar Kano zaman lafiya da karuwar Arijit.

Malam Aminu ya Kara da cewa, gudanar da taron adduoin wani bangare ne na cika umarnin Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusuf Kabir, bisa Umarni da ya bayar na ci gaba da yin adduoi na samu zaman lafiya da cikakken tsaro a jihar Kano da kasa Baki Daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button