Shiyyar Ilimi ta Rano Ta Karrama Shugaban SUBEB Bisa Gudunmawarsa Wajen Bunƙasa Ilimi
Shiyyar Ilimi ta Rano Ta Karrama Shugaban SUBEB Bisa Gudunmawarsa Wajen Bunƙasa Ilimi

Daga M.A Turaki
Shiyyar Ilimi ta Rano ta karrama Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano, Malam Yusuf Kabir, bisa jajircewarsa da gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa harkokin ilimi a jihar.
An gudanar da bikin karramawar ne a ɗakin taro na UK Umar dake garin Rano, inda Shugaban Hukumar, Malam Yusuf Kabir, ya samu wakilcin Daraktan Sashen Lura da Harkokin Sadarwa na SUBEB, Balarabe Danlami Jazuli.
Da yake jawabi a madadin Shugaban Hukumar, Daraktan ya bayyana cewa Hukumar Ilimin Bai Ɗaya na daga cikin hukumomin da Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ke bai wa kulawa ta musamman, domin cika burinta na bunƙasa ilimi a kowane mataki.

Ya ƙara da cewa samar da tsarin shiyyoyin ilimi an yi shi ne domin ƙarfafa duba makarantu da inganta harkokin koyarwa da koyo, tare da tabbatar da ingantaccen kulawa tun daga tushe.
Malam Yusuf Kabir ya yi kira ga al’ummomin ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin Shiyyar Ilimi ta Rano da su ƙara mara wa ƙoƙarin gwamnatin jihar baya domin cimma burin ci gaban ilimi..
Daga bisani, ya miƙa godiyarsa ga Daraktan Shiyyar da dukkan ma’aikatansa bisa shirya wannan muhimmin taro.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Malam Naziru Muhammad Ya’u Rano, ya bayyana karrama ma’aikata da shugabannin makarantu a matsayin abin tarihi da zai ƙara ƙwarin gwiwa ga waɗanda aka karrama tare da sauran ma’aikatan ilimi.
Da ya tabo ayyukan raya ilimi, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya ce Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bullo da tsare-tsare da dama na inganta ilimi, ciki har da ware kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin bana ga fannin ilimi, daukar malamai, da samar da kayan koyo da koyarwa a makarantun jihar.

Ya kuma bayyana cewa Majalisar Ƙaramar Hukumar Rano ta yi nisa wajen rabawa ɗalibai rkayan sawa na makaranta da littattafai da sauran kayan rubutu, domin ƙara inganta ilimi a yankin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar ya yaba wa waɗanda aka karrama, tare da jan hankalinsu da sauran malamai da shugabannin makarantu da su ƙara himma wajen gudanar da ayyukansu.
A jawabansu daban-daban, wakilin Shugaban Kungiyar Malamai ta Jihar Kano, Kwamred Ubale Bala, da kuma Shugaban Zauren Sakataren Ilimi na Jiha kuma Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Garun Malam, Malam Alhaji Sabo Muhammad, sun yaba da tsarin da Ofishin Shiyyar Ilimi ta Rano ya bullo da shi na zakulo waɗanda suka cancanci karramawa, tare da kira ga sauran shiyyoyin da su kwaikwayi wannan tsari.
Tun da farko, Daraktan Shiyyar Ilimi ta Rano, Alhaji Sunusi Uba Ahmad, ya bayyana cewa an yi amfani da hazaka, jajircewa, gaskiya da kyakkyawar gudunmawa a matsayin ma’auni wajen zakulo waɗanda aka karrama.
A yayin taron, an karrama Shugabannin Kwamitocin SBMC, shugabannin makarantun firamare da na ƙananan makarantun sakandare, sarakunan gargajiya, da sauran shugabannin al’umma daga ƙananan hukumomin Rano, Bunkure, Kibiya da Garun Malam, waɗanda ke ƙarƙashin Shiyyar Ilimi ta Rano.





