An bayyana Koyar da Daliban Firamare Harkokin Noma da Kiwo: Matakin hanyar samun Dogaro da Kai a Nan Gaba
An bayyana Koyar da Daliban Firamare Harkokin Noma da Kiwo: Matakin hanyar samun Dogaro da Kai a Nan Gaba

Daga Usman Dau Isa /JB Danlami
A wani muhimmin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da noma da kiwo, Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha (SUBEB) tare da hadin guiwar Hukumar Ilimin Bai Daya ta Kasa (UBEC) ta bayyana kudirinta na tabbatar da cewa daliban makarantun firamare a jihar za su rika koyon harkokin noma da kiwo a matsayin wata muhimmiyar hanya ta gina kansu da samun hanyoyin dogaro da kai tun daga matakin farko na rayuwarsu.
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusif Kabir, ta bakin wakilinsa Daraktan lura da makarantu, Malam Ibrahim Yahuza, ya bayyana hakan yayin taron da aka gudanar a ɗakin taro na SBMC, wanda aka shirya domin ƙarfafa ilimin da sana’o’i a tsakanin daliban firamare ta hanyar koyar da su dabarun noma da kiwo
Ya ce:”Wannan shiri zai ba daliban dama na fahimtar hanyoyin samun sana’a da rayuwa mai inganci, wanda hakan zai taimaka musu kafin su gama karatu, da ma bayan kammalawa, domin su samu mafita daga dogaro da aiki kawai a ofis
Taron ya mayar da hankali ne wajen tattauna hanyoyin da za a koyar da dalibai abubuwan kamar:
Dashen bishiyoyi don kare muhalli da samar da kayan amfanin gona da kiwon kifi, domin inganta abinci da sana’a , sai Kuma Kiwon zomo da tattabara a matsayin sana’o’in gaggawa da riba
Shugaban ya bayyana cewa koyar da irin wannan sana’o’i zai ba dalibai damar samun ƙwarewar da za su iya amfani da ita wajen dogaro da kansu.
A ƙarshe, ya miƙa godiya ga UBEC bisa samar da tallafi da goyon bayan da suka bayar domin gudanar da taron da kuma aiwatar da shirye-shiryen koyar da harkokin noma da kiwo a makarantun firamare, tare da wayar da kai ga masu ruwa da tsaki a LGEA domin tabbatar da nasarar shirin.
Malam Yusif Kabir ya yi amfani da wannan dama ya godewa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif bisa amincewa a shigar da wannan tsari na koyar da dabarun noma da kiwo a makarantun firamare don inganta rayuwa da samar da hamyoyin dogaro da Kai.